Dalilin da yasa na yi kasadar boye kiristoci yayin rikicin Jos - Limamin da ya ceci Kiristoci 200

Dalilin da yasa na yi kasadar boye kiristoci yayin rikicin Jos - Limamin da ya ceci Kiristoci 200

- Malamin addinin nan da ya ceci rayuwar mabiya addinin Kirista a Filato ya bayyana dalilinsa

- Duk da kamarin rikici a jihar ta Filato hakan bai hana shi aikata abin kirki ba

- Malamin yana cigaba da shan yabo a wuraren mutane da dama bisa wannan namijin kokari

A kwanakin baya ne wasu yan bindiga da ba san ko su waye ba suka kai farmaki wasu kananan hukumomi har guda uku a jihar Filato, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100.

Ta fito fili: Limamin da ya sadaukar da ransa don ceton Kiristoci sama da 200 ya bayyana dalilinsa
Ta fito fili: Limamin da ya sadaukar da ransa don ceton Kiristoci sama da 200 ya bayyana dalilinsa

Sai dai wani bawan Allah mai suna Mallam Abdullahi ya ceci rayuwar wasu mabiya addinin Kirista masu yawan gaske, inda ya boye su a wani Masallaci dake kauyen Nghar Yelwa a jihar.

An dai rawaito yadda Limamin ya bayyana batun ceton nasu ne a wata tattaunawa da yayi da jaridar Punch, Mallam Abdullahi mai shekaru 83 a duniya ya sadaukar da rayuwarsa domin cetonsu mutanen, sannan ya sha alwashin cigaba da yin hakan matukar yana raye.

Mallam Abdullahi ya ce ya aikata hakan ne musamman yadda yayi duba da irin rayuwar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi da mutane mabiya addinai daban-daban a lokacinsa.

KU KARANTA: Komai nisan jifa: Makasan Farfesa Halima sun shiga hannun 'yan sanda

"Ina da mata har guda uku amma ragowar sun rasu sai guda daya yanzu, wadda ta kasance ‘yar kabilar Berom ce, kuma daga cikin 'ya'ya 20 dana haifa guda 6 mabiya addinin Kiristanci ne". Limamin ya shaida.

Abdullahi ya cigaba da cewa tunda ya tashi a rayuwar sa bai taba ganin mummanan tashin hankali irin wanda aka yi ba. "Ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba kuma bana fatan sake faruwarsa".

Mallamin ya kara da cewa, "Abinda baka so ayi maka tabbas bai kamata ka yiwa wani ba. Maganar addini ce kuma tsakanin mutum ne da Allah, babu wanda aka bawa damar ya dauki rayukan wasu, duk wannan abubuwan da ake yi babu wanda yake da tabbas zai shiga aljanna sai har kaje kaga abinda ka aikata".

"Ya kamata mu koyi yadda zamu ke daukar rayuwar dan Adam da daraja, bai kamata muke kashe juna ba".

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya zata karrama wannan tsoho bisa wannan aiki da yayi domin samar da cigaban zaman lafiya.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel