Rikicin Taraba: An kashe mutane 4 tare da raunata wasu 8

Rikicin Taraba: An kashe mutane 4 tare da raunata wasu 8

- Da alama rikicin jihar Taraba da sauran rina a kaba

- Sasantawa ta fuskanci cikas bayan sake barkewar harbe-harbe

- Arewa maso tsakiyar kasar nan ta shiga sahun yankuna masu fama da rikice-rikice

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar mutane 4 tare da jikkata wadansu guda 8, gami da kone gidaje masu yawa bisa dalilin daukar fansa a tsakanin al'ummar kunini da ke yankin karamar hukumar Lau.

Ba kanta, rikicin jihar Taraba ya dawo har an sake kashe mutane 8
Ba kanta, rikicin jihar Taraba ya dawo har an sake kashe mutane 8

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Taraba ASP David Misal ne ya tabbatarwa da manema labarai a birnin Jalingo. Ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kashe wadansu mutane guda 2 a lokacin da suka bude musu wuta, su kuma jami'an ‘yan sandan suka mayar da martani.

KU KARANTA: Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda

“A ranar 2 ga Agustan nan ne, rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa an samu wata hatsaniya a lokacin da ake bikin Dodo na al'ada a kauyen Wailawa, hatsaniyar ta faru ne a tsakaninin shugabannin al'ummar yankin wadanda suka hadar da Fulani da kuma Wailawa, inda aka garzaya da mutune 2 da suka samu raunuka zuwa asibiti domin ceton rayukansu" In Ji David Misal.

Jin hakan ya sanya kwamishinan ‘yan sandan na jihar Taraba Mista David Akinremi ya tura jami'an ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a yankin.

“An kirawo shugabanin bangarorin da suke rigima da juna domin magance matsalar, jim kadan da fara tattaunawar sai muka rinka jin karar harbin bindiga yana fitowa daga wani sashe na kauyen, wanda hakan ya kara lalata al'amura"

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng