Duniya sabuwa: Ku zo kuga Sarkin gargajiya a Najeriya da ya yi ikirarin fin Dangote kudi
Wani basaraken gargajiya a yankin Yarbawa watau Oluwo of Iwo land, Oba AbdulRasheed Adewale Akanbi ya fito ya bayyanawa duniya tarin dukiyar sa da kadarorin sa da yake da su.
Haka ma Sarkin yayi ikirarin cewa a duk Najeriya babu mahalukin da ya kai shi kudi ciki kuwa hadda fitaccen mai kudin nan na Najeriya da ma nahiyar afrika baki daya, Alhaji Aliko Dangote.
KU KARANTA: Kwankwaso bai iya cin mazabar sa a 2019 - Ganduje
Legit.ng dai ta samu cewa Sarkin ya zayyana dukkan kadarorin dake a cikin kasar sa a matsayin nashi ciki kuwa hadda na kamfanin Dangote da ma dukkan al'ummar kasar ta sa.
A wani labarin kuma, Shugaban rundunar hukumar hana fasakwaurin kayayyaki a Najeriya watau Hameed Ali ya amince da sauye-sauyen wuraren aiki ga manyan jami'an rundunar watau kwanturola-kwanturola saba'in domin magance cin hanci da kuma karin kyautatuwar aiki.
Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na hukumar Joseph Attah ya fitar a garin Abuja ranar Juma'ar da ta gabata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng