Ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar mutun 1 da rushewar gidaje 40 a Kano
Ruwan sama kamar dab akin kwarya da aka zuba a ranar Alhamis yayi sanadiyan mutuwar mutun daya da kuma lalata gidaje sama da 40 a karamar hukumar Dambatta dake jihar Kano.
Ruwan saman da ya fara zuba daga karfe 4:00 na yamma ya shafe tsawon sa’o’i hudu sannan ya lalata kaya na miliyoyin naira.
Kansilan karamar hukumar, Abdullahi Sani Dambatta, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kano a ranar Juma’a.
KU KARANTA KUMA: Sojin sama sun yi amfani da jirgin yaki sun fatattaki barayin shanu a kusa da kauyukan Yanwari da Mashema a Zamfara
Yace mutun guda ya rasa ransa sakamakon gini da ya rufta a unguwar Makafi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng