Sojin sama sun yi amfani da jirgin yaki sun fatattaki barayin shanu a kusa da kauyukan Yanwari da Mashema a Zamfara
Rundunar sojin sama tace jirgin yakinta ya fatattaki barayin shanu da dama a yayin hare-haren sama da ta kai kauyukan Mashema da Yanwari na jihar Zamfara.
Air Commodore Ibikunle Daramola, daraktan hulda da jama’a da bayanai na rundunar, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 3 ga watan Agusta.
Sun yi wannan gagarumin nasara ne a wani aiki da jami’anta ke gudanarwa a yankin mai suna ‘Operation Diran Mikita’.
KU KARANTA KUMA: 2019: Sauya sheka ba zai hana Buhari cin zabe ba – Tony Momoh
Shirin na daga cikin kokarin da hukumomin tsaron kasar ke yi na son wanzar da zaman lafiya a fadin kasar.
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hugaban hafsan sojin Najeriya, Tukur Buratai ya gargadi kwamandojin rundunar sojin Najeriya kan cewa kada su kuskura su bar gurabensu wajen fuskantar yan ta’addan Boko Haram.
Wannan gargadi na kunshe ne a wata wasika mai kalamai 180 da aka aikewa dukkanin kwamandoji a ko wani mataki, dake gudanar da aiki a guraben da yan ta’addan Boko Haram suka kwashe tsawon shekaru tara suka addaban mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Hakan martani ne kai tsaye da kashe-kashen sojoji da jami’ai da yan ta’addan suka yi a kwanan nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng