Garkuwa da Sheikh Algarkawy: Mun damke mutane biyu - Hukumar yan sanda

Garkuwa da Sheikh Algarkawy: Mun damke mutane biyu - Hukumar yan sanda

An damke mutane biyu game da garkuwa da babban malami, Shaikh Adam Algarkawy, a jihar Kaduna, kakakin hukumar yan sanda, Mukhtar Aliyu, ya bayyana hakan.

Ya bada wannan sanarwa ne bayan kungiyar malamai da limaman jihar Kaduna suka nuna bacin ransu game da wannan abu da ya faru. Kaakakin kungiyar malaman, Dakta Abdullahi Nuhu Maikudi, ya saki jawabin.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa anyi garkuwa da Malam Algarkawy tare da dalibansa ne ranan Alhamis, 2 ga watan Agusta, 2018 a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Wani makusancin malamin da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa babban malamin kan tafi da mutane kimanin 40 amma a ranan sai ya tafi da mutane hudu kacal kuma da su akayi garkuwa.

Yace: "Da ni zasu tafi gonan amma nayi jinkiri, sai na bisu a baya. Kawai sai wasu suka fito suka daukesu, sai na boye a cikin daji don kada su ganni."

“Bayan sun tafi, sai na koma gida domin laburtawa mutane abinda ya faru kuma har yanzu basu tuntubi iyalansu ba."

DSP Aliyu Muktar ya karkare da cewa an zange dantse wajen ceto malamin kuma ana gudanar da bincike.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng