Zaben 2019 zai zama zabe mafi tsada tarihin Najeriya
A wani binciken kwa-kwaf da jaridar Daily Trust ta gudanar game da zabukan shekarar 2019 mai zuwa musamman ma ganin yadda harkokin siyasar ke cigaba da zafafa, ta gano cewa zaben shine zai zama mafi tsada a tarihin Najeriya.
Kamar dai yadda binciken ya nuna, kasafin kudin da shugaba Buhari ya aikewa majalisa na Naira biliyan 242 da za'a kashe wajen gudanar da zaben a tsakanin abunda hukumar INEC din da kuma takwarorin ta tsaro shine mafi yawa da ba'a taba kashewa.
KU KARANTA: Shugaba Kim na Koriya ta Arewa ya aikewa Trump da wasika
A wani labarin kuma, Yayin da lamurran siyasa ke cigaba da daukar sabon salo a jihar Kano da ke a arewa maso yammacin Najeriya, Gwamnan jihar mai ci yanzu, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce tsohon gwamnan kuma Sanata a yanzu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ko a mazabar sa ma ba zai iya lashe zabe ba.
A don haka ne ma gwamnan yace ya kamata ma ya dena mafarkin zama shugaban kasa, lamarin da ya bayyana a matsayin marar yiwuwa ko kadan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng