Mafusatan matasa sun lalata allunan kamfe din Buhari a garin Kano
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya dake a jihar Kano ta fitar da sanarwa tare da kakkausan kashedi ga dukkan masu lalata hotuna da kuma allunan kamfe din shugaba Buhari a jihar.
Mai magana da yawun 'yan sandan na jihar, Musa Majiya ya ce wannan ya zama tilas domin irin yadda mummunar dabi'ar da suke zargin 'yan adawa ne ke yin ta ke man zama ruwan dare a jihar.
KU KARANTA: Yan sanda sun cafke yan kwankwasiya da ke kona tsintsiya a Kano
Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar dai 'yan sandan sun ce sun samu labarin yanzu haka ma wasu bata garin sun lalata allon kamfe din Buhari dake kan titin Sharada kuma sun sha alwashin hukunta duk wanda suka samu da laifin.
A wani labarin kuma Yayin da siyasa a kasar Najeriya ke kara zafafa biyo bayan ficewar da wasu fitattun 'yan siyasa a Najeriya ke yi daga jam'iyyun su zuwa wata domin samun manufofin su daban-daban, wani dan majalisa a jihar Legas yayi wani hasashe.
Dan majalisar dake zaman jigo a jam'iyyar ta APC a jihar Legas mai suna Honorabul Adedotun Adegbola yace duk wadanda suka bar jam'iyyar ta su ta PDP, to tabbas ba wanda zai lashe zaben sa a shekarar 2019 mai zuwa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng