Sauyin sheka: Wani dan majalisa yayi hasashe ga duk wanda ya bar APC

Sauyin sheka: Wani dan majalisa yayi hasashe ga duk wanda ya bar APC

Yayin da siyasa a kasar Najeriya ke kara zafafa biyo bayan ficewar da wasu fitattun 'yan siyasa a Najeriya ke yi daga jam'iyyun su zuwa wata domin samun manufofin su daban-daban, wani dan majalisa a jihar Legas yayi wani hasashe.

Dan majalisar dake zaman jigo a jam'iyyar ta APC a jihar Legas mai suna Honorabul Adedotun Adegbola yace duk wadanda suka bar jam'iyyar ta su ta PDP, to tabbas ba wanda zai lashe zaben sa a shekarar 2019 mai zuwa.

Sauyin sheka: Wani dan majalisa yayi hasashe ga duk wanda ya bar APC
Sauyin sheka: Wani dan majalisa yayi hasashe ga duk wanda ya bar APC

KU KARANTA: Sarkin Kano ya caccaki gwamnatin Buhari

Honorabul Adedotun Adegbola din dai ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da 'yan jarida a garin na Legas inda ya bayar da ansa game da tambayar da aka yi masa.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya dake a jihar Kano ta fitar da sanarwa tare da kakkausan kashedi ga dukkan masu lalata hotuna da kuma allunan kamfe din shugaba Buhari a jihar.

Mai magana da yawun 'yan sandan na jihar, Musa Majiya ya ce wannan ya zama tilas domin irin yadda mummunar dabi'ar da suke zargin 'yan adawa ne ke yin ta ke man zama ruwan dare a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng