Farin jini daga Allah: Matasan yankin Neja Delta sun amince da takarar tazarcen Buhari
Wata kungiyar matasa a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ta Niger Delta Youths, Women and Security Movement for Buhari (NDYW&SMB), a turance jiya ta tabbatar da goyon bayan ta ga takarar tazarcen shugaba Buhari a 2018.
Shugaban kungiyar, Mista Felix Ubokan shine ya sanar da hakan a cikin wata takardar manema labarai da ya fitar inda kuma yace sam ba sun yi haka bane domin wata manufa ta siyasa illa dai tsantsar gaskiyar da suka ga ta fito fili ne.
KU KARANTA: Yan Tijjaniyya sun fitar da sanarwa kan 'yan kungiyar Hakika
Legit.ng ta samu haka zalika cewa Mista Felix ya bayar da samuwar tsaro da kuma ayyukan cigaba da dama a yankin a matsayin abubuwan da suka sa suka yanke wannan shawarar ta su.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ekiti dake a kudu maso yammacin Najeriya, Ayodele Fayose mai barin gado ya shawarci 'yan jihar ta sa da su kwantar da hankalin su tare da bin doka da oda yayin da suke neman hakkin su a gaban kotu na murde masu zaben gwamnan jihar da yace anyi.
Fayose dai ya bayar da wannan shawarar ce a garin Ado Ekiti yayin da ya kai ziyarar duba ayyukan ginin kasuwar garin da akeyi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng