Aiki-ga-mai-kare-ka: Shugaba Muhammadu Buhari zai kafa sabbin ma'aikatu 2
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta shirya tsaf domin kafa sabbin ma'aikatu guda biyu a karkashin babbar ma'akatar dake kula da kimiyya da fasaha watau ministry of Science and Technology a turance.
Mai'aikatun da za'a kafa din dai sune na kwararowar hamada da zaizayar kasa da kuma bincike watau National Agency for Desertification & Erosion Research (NADER) a turance da kuma ta na'urorin zamani watau Research in Robotics & Artificial Intelligence (NARRAI) a turance.
KU KARANTA: Mafusatan matasan sun lakadawa yan APC din da suka canza sheka
A wani labarin kuma, Tsohon shugaban babban bankin tarayyar Najeriya kuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi ya caccakin gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari da kasar Afrika ta kudu bisa kan kin rattaba hannu akan yarjejeniyar kasuwanci a Nahiyar Afrika.
Sarkin yace abun takaici ne ace kasashen Afrika 44 duka sun sanya hannu a takardar amma Najeriya da Afrika ta Kudu sun kekashe kasa sun kiya inda yace ya kamata a sake zama domin lalubo bakin zaren.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng