Dakta Bukola Saraki ya zayyana dalilai 7 da suka sa ya fice daga jam'iyyar APC
Da yammacin yau ne dai shugaban majalisar dattijan Najeriya, Dakta Bukola Saraki ya ayyana barin jam'iyyar sa ta APC mai mulki.
Sai dai a lokacin da ya fitar da sanarwar ficewar ta sa, bai yi karin haske ba sosai kuma bai bayyana wace jam'iyyar zai koma ba.
KU KARANTA: Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya yayi murabus
Legit.ng ta samu cewa daga baya ne yanzu ba da dadewa ba ya zayyana wasu dalilai akalla 7 da yace sune musabbabin ficewar sa jam'iyyar.
Ga su kamar haka:
1. Yace ya fahimci cewa wasu 'yan jam'iyyar basu son zaman lafiya ba kuma su ba kowa darajar sa.
2. Yace haka ma dukkan wasu ginshikan da aka kafa jam'iyyar da su anyi fatali da su.
3. Yace ana cigaba da muzgunawa abokan siyasar sa acikin jam'iyyar tamkar wasu bari marasa gata ko 'yanci.
4. Yace wasu tsiraru a jam'iyyar sun hana duk wani yunkurin da yayi domin ganin an samu daidaito.
5. Yace gwamnatin tarayya kuma ba ta baiwa yan majalisu darajar su.
6. Yace ana yiwa duk wanda ya so kawo gyara ko bayar da shawara kudin goro da cewa ya saci kudin gwamnati ne.
7. Yace gwamnatin APC din tana nema ta mayar da majalisar tarayya 'yan amshin shata kawai.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng