Giggiwa ta sanya wani magidanci ya rinka shararawa matarsa mari har ta mutu

Giggiwa ta sanya wani magidanci ya rinka shararawa matarsa mari har ta mutu

- Zafin zuciya ya kai wani miji ya baro

- Ya hasala ne inda ya takarkare ya zabgawa matarsa marin da sai da ta hango wuta

- Wanda a sanadin marin ta garzaya barzahu, shi kuma tuni kuliya ya yanka maza biza zuwa kurkuku

Alkalin kotun majistiren Ebute Meta da ke jihar Legas ta bayar da umarnin daure wani magidanci mai kimanin shekaru 47 a duniya, magidancin mai suna Premier Imafidon an daure shi ne bisa laifin shararawa matarsa marin da ya kai ga zama ajalinta.

Giggiwa ta sanya wani magidanci ya rinka shararawa matarsa mari har ta mutu
Giggiwa ta sanya wani magidanci ya rinka shararawa matarsa mari har ta mutu

Alkalin kotun mai shari’a A. O Ajibade ta bayar da umarnin garkame Imafidon a gidan yarin Ikoyi tare da umartar da a mika kudin laifin zuwa ga sashen manyan laifuffuka domin zurfafa bincike. Sannan ta dage sauraron shari'ar zuwa 3 ga watan Satumbar.

KU KARANTA: Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda

‘Yar sanda mai gabatar da kara Sajan Maria Dauda, ta bayyanawa kotun cewa Imafidion ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Yuli da milasin karfe bakwai na maraice, a gidansa da ke unguwar Apata a yankin Agege.

Yanzu haka dai na zarginsa ne da aikata laifin kisan kai.

Ta kara da cewa Imafidion ya shararawa matarsa mari inda har ta sheka barzahu, wanda hakan ya sabawa da sashe na 224 na kundin laifuffuka na jihar Legas.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng