Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda

Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda

- Rana dubu ta barawo guda ta mai kaya, in ji masu iya magana

- Yau rana ta kubcewa wani kasurgumin dan kungiyar asiri

- 'Yan sanda sun yi masa kamun Kazae kuku da shi da makamansa

Mataimakin shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa reshen jihar Benin Mista Rasheed Olatunde ya bayyana cewa hukumar tasu ta cafke wani rikakkaen mutum mai suna Wilson Iriajen da ake zargin dan kungiyar asiri ne.

Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda

Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda

Olatunde ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai, inda yace kamen ya biyo bayan umarnin shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa ne domin cigaba da karkade manyan laifuka a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa a lokacin da ake tuhumar mai laifin ya amsa laifinsa tare da bayyana cewa yana daya daga cikin 'yayan kungiyar asiri ta Eiye.

Mai laifin yayi karin haske, inda ya ce ya fara wannan harka ne tun a shekarar 1992 lokacin yana dalibi a Jami'ar Ambrose Ali University, Epkoma, dake jihar Edo.

"Na gaji wannan harka ne daga wajen mahaifina saboda kare kaina, musamman idan ka duba yanayin kasar nan".

"Ni ba barawo bane kawai ina yin kasuwancin saye da sayar da bindigu ne har na tsawon shekaru bakwai, kuma ban taba yin aure ba amma ina da yaro".

KU KARANTA: Hukumar NAFDAC ta dakile wata babbar annoba da aka so shigowa da ita kasar nan

Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Emeka Ihenacho, ya bayyana irin makaman da hukumar ta samu bayan kama shi wanda ya hada da bindiga kirar double barrel mai lamba MBDT 5870, sai wata bindiga samfurin kirar Ingilishi mai lamba T587013-0216 da P630882.

Har wa yau, an same shi da nau'ra mai kwakwalwa kirar kamfani Apple, sai fasfot da kuma kayen maye duk a tare da shi.

Iheanacho ya kara da cewa hukumar ta ‘yan sanda tana kokari wajen ganin ta kawo karshen bara gurbin mutane jihar. Yanzu haka ana cigaba da bincikar mai laifin kuma nan da wani lokaci za’a gurfanar da shi gaban kuliya domin yanke masa hukunci.

Sannan ya tunatar da al'umma cewa alhakin sa ido da tsaro yana kan kowa ba wai hukumar ‘yan sanda kadai ba.

"In har zamu cigaba da samun sahihan bayanai mu kuma zamu cigaba da dakile duk wasu masu aikata miyagun laifuka". Inji kakakin hukumar ta ‘yan sanda na jihar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel