Saraki ya cacaki Abdulahi Adamu, yace sanatan mayaudari, kuma makaryaci ne

Saraki ya cacaki Abdulahi Adamu, yace sanatan mayaudari, kuma makaryaci ne

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Litinin ya bayyana abokin aikinsa kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu a matsayin mayaudari kuma babban makaryaci.

Saraki a caccaki Adamu ne yayinda ya maida martani ga wani furuci da ake zagin Adamu ne ya yi ta.

Anyi zargin cewa Mallam Adamu ya zargi shugaban majalisar attawa da kiran wani sanata, Dino Melaye a matsayin dodo a wata hira da shi. Saraki yayi zargin cewa Adamu ya yi wannan furuci ne a wata hira da jarida.

Saraki ya cacaki Abdulahi Adamu, yace sanatan mayaudari, kuma makaryaci ne

Saraki ya cacaki Abdulahi Adamu, yace sanatan mayaudari, kuma makaryaci ne

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan mazabar Nasarawa ta yamma, ya ce da shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya halarci ganawar sanatocin APC da Buhari a makon jiya, da ya fitittikeshi daga fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ya zama dole mu tsige Ortom Mun – Hon Ikyange

Bayan sanatoci 14 na jam’iyyar APC sun sauya sheka, shugaba Buhari ya gayyaci sauran sanatocin da suka rage fadar shugaban kasa amma an nemi shugaban majalisan an rasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel