Hotuna: Shugaba Buhari ya isa kasar Togo domin halartan taron ECOWAS/ECCAS
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya isa kasar Togo a jiya Lahadi, 29 ga watan Yuli domin halartan taron ECOWAS/ECCAS da za’a yi kasar cikin wannan makon.
Shugaban kasan ya samu kyakkyawan tarbo daga shugaban kasar Togo, Gnassingbe Fraure, da kuma shugaban kasar Liberia, George Weah.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da za su tattauna akai a wannan taron shine zaman lafiya da tabbatar da tsaro. Ya bayyana hakan ne a wani gajeren jawabin da ya saki da safen nan a shafin ra’ayinsa na Tuwita inda yace:
“Zaman lafiya da tsaro ne babban abinda za mu tattauna a kai a taron ECOWAS/ECCAS yau a Lome, Togo. Za mu tattauna yadda za’a samar da mafita daga cikin halin rashin tsaron da muke ciki. Abinda ya tattari tsaro, hada kai a matsayin kasashe duk daya ne da shirye-shiryen gida.”
Legit.ng ta kawo muku rahoton zuwan shugaban kasar Togo Najeriya inda ya gana da shugaba Buhari a jihar Katsina.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng