Iyalan Dasuki sun kai ministan shari'a AGF Malami kara

Iyalan Dasuki sun kai ministan shari'a AGF Malami kara

- Bayar da belin Dasuki da kuma kin amincewa da gwamnatin tarayya keyi ba wani abu ne sabo ba

- Bayan kotunan Najeriya har kotun Nahiyar Afirka ta yamma da tabayar da belinsa da umarnin biyasa miliyoyin kudade a matsayin fansar tauye masa hakki, amma shiru kake ji

- Sai dai a wanann karon iyalansa sun dauki wani mataki da ba lallai ya yiwa ministan shari'a na kasar nan Abubakar Malami dadi ba

Iyalan tsararren tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya sun kai ƙarar babban ministan shari'a na kasa Abubakar Malami zuwa ƙungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) da buƙatar kungiyar ta gudanar da bincike gami da hukunta sa dangane da yadda yake nuna rashin kwarewa a aikinsa tare da furta kalaman da suke nuna yafi karfin doka.

Iyalan Dasuki zasu jawa babban ministan shari'a AGF Malami salalan tsiya
Iyalan Dasuki zasu jawa babban ministan shari'a AGF Malami salalan tsiya

A cikin wasikar da iyalan Dasukin suka aikewa uwar kungiyar ta kasa, sun nemi da lallai-lallai a hukunta Ministan saboda yadda yake yin buris da umarnin kotu.

Wasikar da suka aike mai dauke da kwanan watan ranar 23 ga watan Yunlin da muke ciki, ta kunshi bayani kan yadda Abubakar Malami yayi kalaman da suke na raini ga kotu da sabawa dokar aikinsa wanda kuma hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya sannan kuma cigaba da tauyewa Dasukin hakkinsa na ɗan Adam ne, tun bayan kama shi a watan Disambar shekara ta 2015.

Iyalan sun bukaci lalla-lallai a binciki gwamnatin tarayya dalilin da ya sanya taki bin umarnin kotu bayan kotun ta bayar da Dasukin beli.

Wasikar korafin na dauke da sanya hannun matarsa Binta Dasuki da dansa Abubakar Dasuki da kuma umar Dahiru ɗan gidan amminsa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Daga karshe, Kotu ta baiwa Kanal Sambo Dasuki beli

Sun bayyana yadda aka gurfanar da Dasukin gaban babbar kotin tarayya dake Abuja da ma sauran kotuna bisa zarginsa da laifuka daban-daban amma kotunan suka bayar da shi beli domin zargin da ake masa ba zasu hana bayar da shi belin ba.

In za’a iya tunawa dai a ranar 29 da watan Disambar 2015 ne jami’an tsaro na farin kaya (DSSS) suka kutsa cikin gidan yarin dake Kuje a garin Abuja su kayi awon gaba da Dasukin bayan ya cika sharuddan belin da aka gindaya masa.

Hatta ma dai kotun Nahiyar Afirka ta yamma (ECOWAS) sai da tayi umarnin sakin tsohon sojan a matsayin beli, sannan a biya shi Naira N15m a matsayin kudin fansar tauye masa hakki da akayi. Amma dai shiru kake ji ba wan ba kanin.

Iyalan Dasuki zasu jawa babban ministan shari'a AGF Malami salalan tsiya
Iyalan Dasuki zasu jawa babban ministan shari'a AGF Malami salalan tsiya

Iyalan Dasukin sun bayyana cewa duk wani yunkuri na ganin an shawo kan gwamnatin tarayya don ta bi umarnin kotu amma tayi kunnan uwar shegu da shi.

Kimanin shekaru kusan uku kenan gwamnatin tarayyar na cigaba da tsare Sambo Dasuki ba tare da wata sahihiyar takardar izinin hakan daga kotu ba, in ji iyalansa.

A don haka ne iyalan tsohon mai bawa shugaban kasar shawara suka yi mamakin yadda babban lauya kamar Abubakar Malami dake da lambar girma ta SAN zai na aika irin haka ba tare da bin umarnin doka ba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng