2019: Buhari zai fadi a Kano, Kwankwaso ya mayar da martini ga Amaechi
Bayan sauya shekan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa People’s Democratic Party (PDP), mai magan da yawunsa, Binta Spikin, ta ce shgaba Muhammadu Buhari ba zai labara a Kano ba a 2019.
Ta bayyana wannan ne ga jaridar Premium Times yayinda yake raddi ga jawabin ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Game da cewar jaridar Punch, Amaechi ya bayyana ranan Juma’a cewa Buhari zai lashe zabe a Sokoto, Kano, da Bauchi ko da yana gadon asibiti ne.
Kana ya ce gwamnonin jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da na Kwara, Abdulfatah Ahmed, za su bar APC.
A martaninta, Binta Spikin ta ce sauya shekan Sanata Kwankwaso babban kalubale ne da zaben Buhari a jihar Kano, bal karya APC ne gaba daya.
Tace: “Ina tunanin sauya shekarsa zai shafi zaben 2019 sosai. Bai wa kada APC a jihar Kano ba, sauya shekarsa ya karya jam’iyyar APC.
“Duk abinda gwamnati tayi, babu yadda za’ayi shugaba Buhari ya ci Kano, babu yadda za’ayi.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng