Ba maraya: Hotunan wata tsohuwa mai shekaru 78 dake sana'ar kanikancin motoci

Ba maraya: Hotunan wata tsohuwa mai shekaru 78 dake sana'ar kanikancin motoci

A dai-dai lokacin da da yawa daga cikin sa'annin haihuwar ta suka koma ga mahaliccin su ko kuma suna gida kwance suna jiran wani ya basu, ita kau wannan tsohuwar mai suna Cecilia Wangari rungumar sana'a tayi domin dogaro da kanta.

Ba maraya: Hotunan wata tsohuwa mai shekaru 78 dake sana'ar kanikancin motoci
Ba maraya: Hotunan wata tsohuwa mai shekaru 78 dake sana'ar kanikancin motoci

KU KARANTA: Wata yar Arewa ta haifi 'yan 5

Ita dai Cecilia, kamar yadda muka samu gwana ce kuma kwararra a fannin iya kanikancin motoci da take da basirar sauke injin mota tayi masa fata-fata sannan kuma ta maida ta tada.

Legit.ng ta samu cewa wani abun ban sha'awa da tsohuwar shine kasantuwar ba ta taba zuwa wata makarantar boko ba domin koyon gyaran da yanzu haka ke zaman babbar sana'ar ta.

Yanzu dai tsohuwar tace ita ko nawa za'a bata ba zata yi wani aikin gwamnati ba domin sana'ar ta ta ishe ta domin tana samun rufin asirin ta da ita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng