Rundunar sojin Saman Najeriya ta kara yaye matukan jiragen yaki
Rundunar sojin saman Najeriya Nigerian Air Force (NAF) a ranar Alhamis din da ta gabata ta kara yaye matukan jiragen yaki a makarantar koyon tukin jiragen dake a garin Kainji.
Da yake jawabi a wajen yaye daliban, Hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar da shugaban makarantar Air Vice Marshal Mohammed Idris ya wakilta ya bayyana yaye daliban a matsayin babban cigaba a kasar musamman ma wajen yaki da take yi da 'yan ta'adda.
KU KARANTA: EFCC ta biyo ta kan surukin Obasanjo
A wani labarin kuma, Mataimakin gwamnan jihar kaduna dake a Arewacin Najeriya, Barnabas Bantex a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana kudurin sa na tsayawa takarar kujerar Sanatan jihar ta shiyyar kudancin ta a zaben 2019 mai zuwa.
Barnabas Bantex ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin na Kaduna inda ya bayyana cewa yanzu ya cimma daidaito tsakanin sa da gwamnan jihar game da kudurin nasa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng