‘Yan bindiga sun kashe mutane 20 a yayinda suke Sallar Isha'i a jihar Zamfara
- Matsalar tsaro na cigaba da ta'azzara a jihar Zamfara
- kullum 'yan bindiga na lababowa suna kashe jami'an tsaro da mutanan gari
- A jiya ma 'yan bindigar sun kashe wasu masallata basu ji ba basu gani ba
Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kashe a kalla mutane hudu a wani masallaci dake kauyen Kwaddi na karamar hukumar Zurmi a yayin da suke tsaka da gudanar da sallar Isha'i da misalin karfe 8:00 pm na dare kuma mutane 8 suka samu rauni.
Mai magana da yawun rundunar ''yan sanda na jihar Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.
'Yan bidigar da har ya zuwa yanzu ba’a kai ga gane ko su wanene ba, sun shigo kauyen inda suka rinka harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da munanan raunuka ga wasu.
KU KARANTA: Jihar Zamfara zata samu sauki: Masu garkuwa da mutane 4 da makamasu sun shiga hannun ‘yan sanda
Kauyen na Kwaddi dai a zagaye yake da daji kuma yayi iyaka da jamhuriyar Nijar, wanda ya sanya abu ne mai wahala ga jami'an tsaro su kai dauki a kowane lokaci da bukatar hakan ta taso, a cewar kakakin rundunar Shehu.
Ya kara da cewa yanzu haka an kai jami'an tsaro yanki domin kare aukuwar lamari makamancin haka tare da tabbatar da komai ya dawo yadda yake.
A satin da ya gabata ma sai da wasu yan bindiga suka kai farmaki a kauyen Gidan Goga wanda yayi sanadin mutuwar akalla mutane uku duk dai a jihar ta Zamfara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng