Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn

Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn

- Hukumar hana fasa kwauri ta kasa na cigaba da samun nasarar dakile shigo da kaya ba bisa ka'ida ba ta iyakokin kasar nan

- Wannan karon hukumar ta sake yin gagarumar nasarar cafke wasu kayan makudan Nairori

Hukumar hana fasa kauri ta kasa Kwastam ta yi nasarar kama wasu motoci makare da maganin nan da aka haramta shigowa da sarrafa shi na Kodin makare a wata babbar mota da tirela cike da shinkafar kasar waje da sauran kayan kasashen waje wanda kimar kudin da za a biya musu do shigowa da su cikin kasar nan ya kai kimanin biliyan 1.12.

Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn
Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn

Kwantirolan hukumar mai kula da shiyyar (A) Mohammed Uba Garba ne ya shaidawa manema labarai wannan nasara a garin Legas.

Wasu daga cikin kayyayakin da aka kama sun hada da katan 498 na maganin Codeine, sai buhun shinkafa ta kasar waje har guda dubu 9,504 (Tirela 15), sai man girki na gwangwani guda 436, katan 333 na daskararrun kayan amfani, sai dilar gwanjon kaya guda 287, da kwancen tayar mota guda 198.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 20 a yayinda suke Sallar Isha'i a jihar Zamfara

Kwantirolan yace karkashin umarnin shugaban hukumar fasa kaurin ta kasa bisa umarnin shugaban kasa, in har an kama irin wadannan kayayyaki za’a ne raba su ne ga 'yan gudun hijira dake Maiduguri.

Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn
Hukumar Kwastam ta kama babbar mota makare da Kodin da motocin alfarma na Naira N1.12bn

Sannan ya umarci masu motocin da aka kama kayan da su da su bayyana gaban hukumar domin karbar kayansu ko kuma su rasa su baki daya.

Ya ce "Hakkinmu ne mu taimakawa wannan gwamnati wajen ganin an taimaki masu noman shinkafa ‘yar gida, wanda hakan zai taimaka wajen rage rashin aikin yi ga matasa".

"Ragowar kayayyakin da aka kama su zamu mika su ga hukumar NAFDAC domin amsa tambayoyi tare da mika su gaban kotu domin yi musu hukunci bisa kin bin dokar da kasa ta shimfida."

Ko baya ma Legit.ng ta rawaito cewa a ranar 6 ga watan Maris ne Hukumar ta danka wasu kudade kimanin Dalar amurka dubu 375,000USD tare da wani mutum mai suna Adamu Rabiu Muhammad mai lambar fasfo A50280997 ga hukumar yaki da cin-hanci da rashawa shiyyar jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel