Masu zanga-zangar adawa da komawar gwamnansu APC sun mamaye ofishin jam’iyyar
Wasu matasa daga jihar Kuros Riba sun yi zanga-zangar nuna adawa da kudirin gwamnan jiharsu, Farfesa Ben Ayade, ta komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewar basu yarda Farfesa Ayade ya koma APC ba saboda zai dawo ne bayan jam’iyyarsa ta PDP ta juya masa baya saboda ya gaza cika alkawuran day a dauka kafin zabensa a skekarar 2015.
Saidai wani daga cikin shugabannin APC da suka samu a ofishinta na kasa dake Abuja ya ga baikon matasan dake zanga-zangar tare da tamnbayarsu me yasa zasu yi zanga-zangar shigowar wani gwamna jam’iyyar yayin da basu yi zanga-zangar ficewar gwamna Ortom na Benuwe daga jam’iyyar ba.
Kakakin masu zanga-zngar, Sankara Unung, ya shaidawa manema labarai cewar basa son APC ta karbi gwamna Ayade tare da bayyana cewar babu gurbin mutane irinsa, da basa iya cika alkawari, a jam’iyyar.
DUBA WANNAN: 2019: INEC ta nada sabbin kwamishinoni a jihohin arewa 2, kalli hotunan rantsuwarsu da Qur'ani
An dade ana rade-radin cewar gwamnan na jihar Kuros Riba na sansana jam’iyyar APC domin ko a wani rahoto da kafafen yada labarai suka wallafa, an jiyo gwamna Ayade na kiran ‘yan majalisar da suka bar APC da marasa kima da gaskiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng