Hayaniya ta kaure yayin da kwamishinoni ‘Yan sanda 2 su ka bayyana don maye gurbin Kwamishina
- Makuwa ko kuskuren lissafi ya sanya an nada kwamishinonin 'yan sanda biyu a jiha daya
- Yanzu haka daya har ya kama aiki yayin da dayan yake daf da zuwa
An samu kaurewar wata hatsaniya a ofishin rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Bayelsa kan rashin sanin waye takamaiman sabon kwamishinan ‘Yan sandan na Jihar.
Rahotanin sun bayyana cewa an samu hatsaniyar ne biyo bayan samun chanjin aiki da aka yiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Don Awunah tare kuma da maye gurbinsa da kwamishinoni guda biyu maimakon daya.
Rahotannin da Sahara Reporters suka rawaito ya bayyana tsohon kwamishinan 'yan sanda Awunah a matsayin daya daga cikin kwamishinan' yan sanda mafi kwarewa dake da nasarori da dama a cikin tarihin aikisa.
Sai dai maye gurbinsa a dalilin sauyin wurin aiki ya haifar da rudani, saboda yadda aka umarci kwamishinan 'yan sanda Joseph Mokain a ranar Litinin da ya karbai aiki daga gare shi, a bangare daya kuma aka sake tura wani kwamishinan' yan sanda, Mohammed Bello a ranar Talata domin shi ma ya maye gurbin duk cikin awanni 48.
KU KARANTA: Bidiyon yadda ‘Yan sanda su ka mamaye gidan Bukola Saraki kafin ya sulale
Wannan yana zuwa ne bisa dalilan rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin gwamna Seriake Dickson da tsohon gwamnan jihar Timipre Sylva.
Tun asali dai akwai takun saka tsakanin gwamna Dickson da kuma Joseph Mokain din, wanda hakan ya sanya ake kallon kawo shi din na da nasaba da tsamin dangantakarsu.
Rashin zuwan kwamishina Bello akan lokaci, saboda bai kammala aikin da yake yi na musamman a jihar Ekiti ba ya sanya Joseph Mokain isa jihar ta Bayelsa a ranar Talatar nan domin kama aiki.
Har kawo wannan lokaci rundunar ‘Yan sanda ta kasa ba ta bayyana matsayinta game da wannan abu mai kama da kuskuran lissafi ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng