Canza sheka: Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharadin zaman lafiya

Canza sheka: Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharadin zaman lafiya

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi wa takwaran sa duk dai a jihar, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso maraba da dawowar sa jam'iyyar PDP tare da bayyana lamarin da cewa abun murna ne.

Sai dai kuma Shekaru din ya bayyana cewa dole ne Kwankwaso yayi biyayya ga jagororin jam'iyyar a jihar idan dai har yana so ya samu zaman lafiya da salama.

Canza sheka: Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharadin zaman lafiya
Canza sheka: Shekarau ya gindayawa Kwankwaso sharadin zaman lafiya

KU KARANTA: PDP ta fitar da jadawalin ranakun zabukan fitar da gwanin ta

Legit.ng ta samu cewa Shekarau din wanda yayi magana ta bakin mai taimaka masa ta bangaren yada labarai, Sule Ya'u Sule, ya ce suna fatan dai Kwankwason ya canza halin sa kuma zai daratta duk shugabannin jam'iyyar da ya tadda.

A wani labarin kuma, Hadaddiyar kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya watau Christian Association of Nigeria (CAN) ta gargadi fadar shugaban kasa da sauran jami'an tsaro da cewa su bi ahankali kar su jefa demokradiyyar kasar cikin rikici.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne jim kadan bayan wani samame da sanyin safiyar jiya da jami'an 'yan sandan Najeriya suka kai a gidan shugabannin majalisar dattijai, Dakta Bukola Saraki da mataimakin sa Ike Ekweremadu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel