Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta fitar da jadawalin ranakun fitar da 'yan takarar ta

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta fitar da jadawalin ranakun fitar da 'yan takarar ta

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party ta fitar da jadawalin ranakun da za ta fitar da 'yan takarar ta da za su shiga zaben 2019 tun daga kan 'yan majalisun jiha zuwa shugaban kasa.

Kamar yadda muka samu, jam'iyyar ta sanya ranakun Juma'a 5 ga wata zuwa Asabar, 6 ga watan Oktoba a matsayin ranakun zaben fitar da gwani na 'yan takarar shugaban kasa.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta fitar da jadawalin ranakun fitar da 'yan takarar ta

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta fitar da jadawalin ranakun fitar da 'yan takarar ta

KU KARANTA: Wani dan kudu ya ba Buhari motocin kamfe din 2019 guda 31

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar dauke da sa hannun shugaban ta na kasa, Prince Uche Secondus a ranar Litinin din da ta gabata.

Haka ma kuma jam'iyyar ta bayyana cewa za ta yi zabukan fitar da gwanin sauran 'yan takara a jam'iyyar a dukkan matakai daga dan majalisar jiha zuwa gwamna daga rana Asabar 15 ga watan Satumba zuwa Juma'a 28 ga watan Satumba mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel