Gwamnatin APC ba su da alkawari – R-APC
Kungiyar sabuwar APC a ranar Lahadi, ta caccaki gwamnatin Buhari, cewa ba su da alkawari.
Ta ce “Gwamnatin nan bata da alkawari ko kadan sannan wasu alkawaran da aka dauka yayi neman zaben APC sun zama kanzon kurege.
“Shugaban kasar wadda ya boye kansa a cikin fadar Villa ya canja lokaci guda yana ta bude kofofin tattaunawa duk sake neman takara."
Kungiyar ta R-APC ka bukaci mambobin ta da su tsaya kan bakarsu na kare martabarsu da kuma daukar matakin da ya kamata waje kare damokradiya.
Kungiyar ta fadama mabobinta a fadin kasa cewa suna nan akan bakarsu babu dadin baki, barazana ko tozarci da zai sasu saukowa daga tubalinsu na son ceto damokradiyya.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki
Sai dai bayanai sun nuna cewa a ranar Lahadi, APC ta gana da shugabannin R-APC, ciki harda Alhaji Buba Galadima.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng