Kada kayi wasa da bindin zaki, saboda za kayi nadama har abada – Shugaban kasar Iran ga Trump na Amurka

Kada kayi wasa da bindin zaki, saboda za kayi nadama har abada – Shugaban kasar Iran ga Trump na Amurka

Shugaban kasa Iran, Hassan Rouhani, ya gargadi takwararsa na Amurka, Donald Trump, kan take-taken da yake masa.

Rouhani ya ja kunnen Trump kan kokarin tada hankalin kasarsa inda ya ce fito-na-fito da kasar Iran uwar dukkan yakoki ne kuma ba za tayi kyau ba.

A ranan lahadin da ya gabata, Hassan Rouhani yace: "Kada kayi wasa da bindin Zaki, inda bah aka a za kayi nadama”.

Ya yi wannan magana ne domin jaddadawa kasar Amurka cewa bata isa ta hana Iran sayar da danyen manta da sauran kasashen duniya ba.

Ya kara da cewa: “ Zaman lafiya da Iran babban zaman lafiya ne da kowa, hakazalika yaki da Iran uwar yakoki ne,”

Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta fita daga yarjejeniyar da gwamnatin da ta gabaceta tayi da sauran kasashen duniya kan karfin nukiliyar kasar Iran.

Sauran kasashen duniya sun soki wannan ab da Amurka tayi sun lashi takobin ba zasu fita ba. Daga cikin kasashen sune Ingila, Faransa, Jamus, Rasha, Sin da gamayyar kasashen Turai.

Tun daga lokacin kasar Amurka ta lashin takobin dawo da takunkumin da ta sanya kasar Iran na kokarin dukufar da tattalin arzikinta. Daya daga cikin wadannan takunkumi shine kokarin hanata fitar da arzikin man fetur dinta sauran kasashen duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng