Dandalin Kannywood: Sadiya Gyale ta karyata labarin mutuwar ta

Dandalin Kannywood: Sadiya Gyale ta karyata labarin mutuwar ta

Daya daga cikin tsaffin fitattun fuskoki na farko-farko a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Sadiya Gyale ta fito ta karyata rade-raden labarin mutuwar ta da aka rika yadawa a kafafen sadarwar zamani a karshen makon da ya gabata.

Da take maida ba'asi game da labarin lokacin da wakilin majiyar mu na BBC ya tambayeta, tsohuwar jarumar ta ce ita lafiyar ta kalau kuma ita ma tana zaune ke kawai sai ta rika jin kiraye-kirayen waya daga 'yan uwa da abokan arziki kan lamarin.

Dandalin Kannywood: Sadiya Gyale ta karyata labarin mutuwar ta
Dandalin Kannywood: Sadiya Gyale ta karyata labarin mutuwar ta

KU KARANTA: Sunayen jaruman fim din Hausa maza 5 da suka fi kowa tsada

Legit.ng ta samu cewa Sadiya ta kara da cewa tun tana daukar abun wasa har dai ta gane cewa lallai labarin karyar na mutuwar tata ya yadu sosai duba da irin yawan mutanen da suka rika kiran nata.

Sai dai jarumar ta bayyana cewa ita ko kusa hankalin ta bai tashi ba bayan faruwar hakan domin ta san dukkan mai rai zai zama gawa wata rana don haka take kara baiwa masoyanta tabbacin cewa tana nan da ranta kuma cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng