Sha’anin tsaro na nema ya gagari hukuma a Jihar Kaduna

Sha’anin tsaro na nema ya gagari hukuma a Jihar Kaduna

A halin yanzu mutane da dama su na kokawa a kan yadda harkar tsaro ya sukurkuce baki daya musamman a Jihar Kaduna. A yanzu fashi da makami da sata da garkuwa da mutane yayi kamari.

Sha’anin tsaro na nema ya gagari hukuma a Jihar Kaduna
Harkar tsaro ya kama hanyar tabarbarewa a Kaduna

Fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna na nema ya zama ruwan dare a cikin ‘yan kwanakin nan, duk da Jami’an tsaron da aka baza a hanyar, ana tare mutane har da yamma ana yi masu fashi a wannan babban titi.

Fashi da makamin har ya kai cikin Gari inda aka addabi jama’a musamman a hanyar zuwa filin jirgin sama. Duk da cewa akwai Makarantar Sojin Najeriya a daf da wannan wuri, bai hana irin ta’adin da ake yi ba dare da rana.

KU KARANTA: Yan bindiga sun harbe babban limami a jihar Filato

Yanzu ma dai mun ji cewa za a rike rufe filin jirgin saman da zarar yamma tayi. Haka kuma ana kukan satar jama’a ana garkuwa da su a hanyoyi da kauyuka. Akwai kuma rikicin Makiyaya da masu ta’adi a irin su Birnin Gwari.

Bayan nan ana kuma dai gamuwa da barazanar tsaro a hanyar zuwa tashan jirgin kasa da ke cikin Garin Kaduna. Mutane sun koka da yadda Jami’an tsaro su ka gagara yin maganin mau yin wannan barna duk da cewa an san inda su ke.

A baya kun ji rikicin Makiyaya ya jawo rasuwar dinbin mutane a Arewacin Najeriya a Gwamnatin Buhari. An hallaka mutane 579 a cikin ‘dan kankanin lokaci a Jihohi 4 a Najeriya. Jihohin su ne Filato, Nasarawa, Kogi, da Benuwai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: