Najeriya ta kara samun zakakuran matukan jiragen yaki

Najeriya ta kara samun zakakuran matukan jiragen yaki

Rundunar sojin saman Najeriya Nigerian Air Force (NAF) a ranar Alhamis din da ta gabata ta kara yaye matukan jiragen yaki a makarantar koyon tukin jiragen dake a garin Kainji.

Da yake jawabi a wajen yaye daliban, Hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar da shugaban makarantar Air Vice Marshal Mohammed Idris ya wakilta ya bayyana yaye daliban a matsayin babban cigaba a kasar musamman ma wajen yaki da take yi da 'yan ta'adda.

Najeriya ta kara samun zakakuran matukan jiragen yaki
Najeriya ta kara samun zakakuran matukan jiragen yaki

KU KARANTA: An soma hada-hadar kudaden Yuan na kasar SIn a Najeriya

A wani labarin kuma, Dakarun sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force (NAF) ta ce rundunar ta ta shirin ko ta kwana ta musamman dake a karkashin babbar rundunar Operation Lafiya Dole sun yi nasarar yin raga-raga da 'yan ta'addan Boko Haram a kauyukan Bulagalaye da kuma Kwakwa, dukan su a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, AVM Olatokunbo Adesanya shine ya sanarwa da manema labarai hakan a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel