Ku sadu da Abdulkarim Dauda Daura, babban mai tsaron lafiyar Shugaba Buhari

Ku sadu da Abdulkarim Dauda Daura, babban mai tsaron lafiyar Shugaba Buhari

Ofishin babban mai tsaron lafiyar shugaban kasa dai watau Chief Personal Security Officer (CPSO) a turance, shugaba Jonathan ne aka ce ya kirkire shi domin samar wa wani na kusa da shi gurbin zama tare da shi sadda yana mulki.

To shi ma dai Shugaba Muhammadu Buhari da ya zo ance sai kawai bai soke ofishin ba shima sai ya kawo wani dan uwan sa na jini, mai suna Abdulkarim Dauda Daura.

Ku sadu da Abdulkarim Dauda Daura, babban mai tsaron lafiyar Shugaba Buhari
Ku sadu da Abdulkarim Dauda Daura, babban mai tsaron lafiyar Shugaba Buhari

KU KARANTA: Buhari ya yaudari talakan Najeriya - Turaki

Legit.ng ta samu cewa Abdulhakim Dauda Daura da ne ga Marigayi Dauda Daura wanda ke zaman yaya ga shugaba Buhari da akace ya taba rike shugaba Buhari din bayan rasuwar mahaifin sa.

Abdulhakim Dauda dai yayi karatun sa ne na digirin farko a jami'ar Ahmadu Bello dake a Zari'a akan aikin gwamnatin sannan kuma ya karatun Difloma a kan harkokin siyasa a kasar Ingila.

An ce ya soma aikin dan sanda ne a shekarar 1985 kuma yayi aiki a jahohi da dama da suka hada da Sokoto, Katsina, Legas, Edo, Kano, Kaduna da kuma Abuja kafin daga bisani yakai matsayin kwamishinan 'yan sanda sannan a 2018.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng