Tiryan-tiryan: Yadda hukumar zabe ta INEC ta kuduri aniyar lakume Naira biliyan 242.44 a zabukan 2019

Tiryan-tiryan: Yadda hukumar zabe ta INEC ta kuduri aniyar lakume Naira biliyan 242.44 a zabukan 2019

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta INEC ta fitar da jadawali dalla-dalla yadda ta kuduri aniyar kashe zunzurutun kudaden da ta bukata domin gudanar da sahihin zabe a 2019 na Naira biliyan 242.44.

Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiki da sabon kasafin kudi na cike gibi zuwa ga majalisar tarayyar kasar inda ya bukaci su amince da shi kamar dai yadda muka samu.

Tiryan-tiryan: Yadda hukumar zabe ta INEC ta kuduri aniyar lakume Naira biliyan 242.44 a zabukan 2019
Tiryan-tiryan: Yadda hukumar zabe ta INEC ta kuduri aniyar lakume Naira biliyan 242.44 a zabukan 2019

KU KARANTA: Jega ya fallasa babbar matsalar 'yan siyasar Najeriya

Legit.ng ta samu cewa yadda aka kasafta kudaden gudanar da zabukan dai shine ita kanta hukumar zaben zata lakume Naira biliyan 189.20 ne a tsakanin shire-shire da kuma biyan ma'aikatan ta na din-din-din da kuma wucin gadi.

Wasu daga cikin wadanda za su anfana da kasafin kudin sune ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro da zai lakume Naira biliyan 4.28 sa kuma jami'an tsaro na farin kaya da za su lakume Naira biliyan 12.21.

Sauran wadanda za su anfana da kudin sun hada da hukumar hukumar tsaro ta sirri da zata anfana da Naira biliyan 2.6 sai kuma jami'an yan sanda da za su kashe Naira biliyan 30.54 sai kuma 'yan sandan farar hula da za su kashe Naira biliyan 3.57.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng