Buhari ya sha alwashin farfado da masakun Arewa da dalar gyada a Kano

Buhari ya sha alwashin farfado da masakun Arewa da dalar gyada a Kano

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta ce tuni ta soma shire-shiren ta na maido da martabar Arewa musamman ma noma da kuma masana'antu irin masaku da kuma dalar gyada a garin Kano.

Kamar dai yadda babban Sakataren masana'antu da kasuwanci, Edet Akpan da Hajiya Aisha Abubakar ta wakilta ta ce, matakin farko da gwamnatin ta dauka shine na bude ofishin shiyya na kula tare da bincike kan harkokin noma na Nigeria Agribusiness and Agro-Industry Development Initiative (NAADI) a jihar ta Kano.

Buhari ya sha alwashin farfado da masakun Arewa da dalar gyada a Kano

Buhari ya sha alwashin farfado da masakun Arewa da dalar gyada a Kano

KU KARANTA: Tsarabar ayyukan cigaba 3 da Buhari ya samo daga kasar Holland

Legit.ng ta samu cewa wakiliyan ta bayyana cewa nan da dan lokaci kadan ne dai ake sa ran kwalliya zata biya kudin sabulu musamman wajen habaka harkokin noma a yankin.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Taraba dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan, Mista Darius Ishaku ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirya makarkashiyar hana shi tare da wasu gwamnoni 6 sake tsayawa takara a 2019.

Darius Ishaku ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a gidan gwamnatin jihar, garin Jalingo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel