Yanzu Yanzu: Buhari ya nada tsohon mataimakin gwamnan CBN, Lemo a matsayin shuaban FERMA
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Tunde Lemo a matsayin shugaban hukumar kula da agajin gaggawa na kan hanya.
Buhari ya nada sabon manajan darakta tare da mambobin hukumar FERMA uda shida.
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya karanta wata wasika da shugaban kasar aika a aban majalisa a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuli inda ya nemi amincewar yan majalisan akan nade-naden.
KU KARANTA KUMA: PDP ta kulla yarjejeniya da Saraki da wasu gwamnoni 3
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kokarin kawo cikas a zaben 2019.
Buhari, a wata wasika da ya akewa majalisar dokoki a ranar Talata, ya bukaci a tura N228.8bn na sabbin ayyukan da majalisar dokoki ta kara a kasafin kudin 2018, domin daukar nauyin zaben 2018.
Kudin gudanar da zabe zai kama N242.4bn. kudin ayyukan da aka kara a kasafin kudin 2018 baki daya N578.3bn.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng