Camfe-camfe 10 da 'yan Najeriya suka aura, suka dauka wai gaskiya ne

Camfe-camfe 10 da 'yan Najeriya suka aura, suka dauka wai gaskiya ne

- Tashi a kasar Najeriya, akwai wasu lokutan da iyaye ke shirya karyayyaki ga yayan su. Wadannan karyayyaki suna tasiri a zukatan yara

- Duk da dai karairayin kan banbanta a yarika da dama, a inda zaka samu na Hausawa daban da na yarbawa

- Wani saurayi mai suna Tunde, manajan saida saide ne a Mansard ya lissafo camfe camfe guda goma da yan Najeriya suka yarda dasu

Camfe-camfe 10 da 'yan Najeriya suka aura, suka dauka wai gaskiya ne
Camfe-camfe 10 da 'yan Najeriya suka aura, suka dauka wai gaskiya ne

Tashi a kasar Najeriya, akwai wasu lokutan da iyaye ke shirya karyayyaki ga yayan su. Wadannan karyayyaki suna tasiri a zukatan yara.

Duk da dai karairayin kan banbanta a yarika da dama, a inda zaka samu na Hausawa daban da na yarbawa.

Wani saurayi mai suna Tunde, manajan saida saide ne a Mansard ya lissafo camfe camfe guda goma da yan Najeriya suka yarda dasu.

1. Dukan namiji da tsintsiya ta taba tana iya hana shi aure.

2. In har yan kungiyar wasan kwallon mu suka saka fararen rigunan kwallo, mukan rasa wasan.

3. Fito da dare yana kiran macizai da shaidanun aljanu.

4. Idan ka saka gashin idonka a takalman iyayen ka, zasu manta da laifin ka.

5. Ba a shan ruwa kwakwa, yana kawo dakikanci.

DUBA WANNAN: Wai wani alkali zai kama shugaban INEC

6. Idan ana ruwa kuma rana ta fito, toh zakanya ce take haihuwa.

7. Idan hakorinka ya cire, ka wurga shi saman rufin daki, kadangare zai dauka sai ya baka wani.

8. Wanda kesa kafa a bango yayin barci, toh yana tarar mayu ne.

9. Idan mutum ya tsallake mace mai ciki, toh yaron zai yi kama dashi.

10. Idan mutum ya zubar da miyau a kasa wani yazo ya tsallake, sai ya samu ciwon makogwaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng