Mutane 30 sun mutu yayinda 7 suka bata a sabbin hare-haren Zamfara

Mutane 30 sun mutu yayinda 7 suka bata a sabbin hare-haren Zamfara

Wasu yan fashi sun kashe akalla mutane 30 a wasu hare-hare da suka kai kauyuka biyar na yankin Gidan Goga dake karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa yan fashin sun kai farmaki kauyukan Sakkida, Farin Zare, Orawa, Gyadde da Sabon Gari akan babura inda suke ta harbin mutane, suna kashe mutane sannan su kwashe dabbobinsu.

Sun ce har yanzu basu san inda wasu mutane bakwai suka shiga ba inda suka kara da cewa babu mamaki sun nutse a cikin ruwa yayinda suke kokarin ketare kogi don tsira.

Mutane 30 sun mutu yayinda 7 suka bata a sabbin hare-haren Zamfara

Mutane 30 sun mutu yayinda 7 suka bata a sabbin hare-haren Zamfara

Sai dai kuma yan sanda a jihar sunce mutane uku aka kashe a kauyukan Sakkida da Gyadde inda suka ce sun dakile duk wani hari ta hanyar fafatawa da yan bangan.

KU KARANTA KUMA: Tsare-tsarenka na iya kawo sauyi a Najeriya – IBB ga Turaki

Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu yace tawagar yan sanda da hadin gwiwar soji sun hadu sun amsa kira kan lokaci sannan yan fashin suka tsere a lokacin da suka iso bayan sun kashe mutane uku.

Shehu ya kara da cewa rundunar ta dakile hari a kauyen Dangebe dake karamar hukumar Zurmi na jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel