Jerin wasu Gwamnonin da ke daf da barin Jam’iyyar APC
Wannan karo mun kawo maku jerin wasu Gwamnonin da yanzu alamu su ka nuna cewa daf su ke da su bar Jam’iyyar APC mai mulki. Ba mamaki Gwamnonin su koma Jam’iyyar adawa ta PDP.
Duka Gwamnonin dai daga Yankin Arewa su ke. Daga cikin Gwamnonin nan dai akwai tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya wanda asalin sa da ‘Dan PDP ne da kuma wani Gwamna wanda shi ma ya dade yana mulki.
1. Gwamnan Benuwai
Gwamna Ortom dai ya samu matsala da Uban gidan sa a siyasa kuma ya nunawa Duniya shi fa tuni APC ta ba shi jan kati. Samuel Ortom dai na iya komawa Jam’iyyar PDP yayi takarar zaben 2019 bisa dukkan alamu.
KU KARANTA: Kasar Amurka ta ba Fayose gaskiya a zaben Gwamnan Ekiti
2. Gwamnan Sokoto
Aminu Waziri Tambuwal yana ta tattaunawa da manyan PDP kuma tun can tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayyar ya bayyana cewa yana tuntubar mafitar siyasar sa inda ya kori wasu Kwamishinonin sa.
3. Gwamnan Kwara
Gwamna Abdulfatahi Ahmed yana cikin Gwamnonin da su ka bar Jam’iyyar PDP a 2014. Yanzu haka dai shi ma Gwamnan na Kwara yana kus-kus din tserewa daga APC. Watakila Gwamnan da Bukola Saraki su koma PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng