Bene mai hawa 4 ya rugurguzo kasa a jihar Anambra

Bene mai hawa 4 ya rugurguzo kasa a jihar Anambra

- Mutanen wani yanki a jihar Anambra sun shiga mamaki bayan rushewar wani ginin bene

- Abin yazo da sauki ne bayan an gano babu kowa a cikinsa

- Ya zuwa yanzu dai mahukunta a yankin na kira ga gwamnati da ta bincika don gano musabbabin rugujewarsa

Wani gini mai dauke da bangarori guda hudu ya rushe a yankin Owelle-aja dake karamar hukumar Idemili ta arewacin jihar Anambra, amma babu wanda suka jikkata ko suka samu rauni.

Ginin bene mai hawa 4 ya rugurguzo kasa a jihar Anambra
Ginin bene mai hawa 4 ya rugurguzo kasa a jihar Anambra

Wannan gini mai dauke da benaye manya guda hudu dake kan titin Tony Eze, rahotonni sun gabata cewa ya rushe ne da misalin karfe 7 na safe.

Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa ginin ya ruguje ne yayinda babu kowa a cikinsa, sakamakon ma'aikatan dake aikin ginin ba su zo ba a lokacin.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a boye sunansa, ya kalubalanci mamallakin ginin, inda yace gini an tsara za a gina shi hawa biyu ne wanda daga baya mai shi ya bada umarnin a kara hawa biyu akai wanda yake ganin wannan shi ne dalilin da yasa ginin ya rushe.

Wata majiya ta bayyana cewa kafin rushewar ginin an ga wasu wurare na ginin ya nuna gazawa ta hanyar tsagewar bango.

KU KARANTA: Makiyaya sun damke barayin shanayensu yayinda suka kawo kasuwa sayarwa, sun kashe su nan take

Obiageli Okaforuzu, wanda tana daya daga mazauna yankin ta ce ginin ya dauki tsawon shekaru ana yinsa ba tare da an gama ba.

"Mun godewa Allah lokacin da abun ya faru babu kowa a ciki, da yanzu wani labari na daban ake yi" kamar yadda ta bayyana.

Shugaban dillancin filaye da gidaje na yankin Chuka Chukwudebelu, ya bayyana damuwarsa game da faruwar lamarin inda ya bukaci gwamnati ta tura wakilai domin ganin abinda ya faru da kuma nemo dalilin faruwa hakan.

Shi ma daga bangarensa shugaban tsara gine-gine na jihar mista Joachim Ulasi ya nuna damuwarsa akan mutanen da basa neman shaidar yin gini a hukumance da amfani da kayan gini marasa kyau wanda ya ce hakan yana da alaka da rushewar ginin.

Sannan ya ja hankalin mutane tare da nuna muhimmancin hukumar wajen sa ido game da gine-gine.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng