Gwamna Ortom ya watsawa APC kasa a ido yayinda ake kokarin sulhu da shi
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya watsawa jam’iyyar APC kasa a ido yayinda ya ki amsa sammacin da shugabancin jam’iyyar tayi masa tare da tsohon uban gidansa, George Akume, a sakatariyar jam’iyyar.
Shi Akume ya masa goron gayyatar inda suka tattauna da mataimakin shugaban jam’iyyar, Sanata Lawal Shaiubu, kan yadda za’a samu mafita daga cikin rikicin da ke tsakaninsu da Ortom.
Wani makusancin gwamnan ya bayyanawa jaridar Thusday a Abuja cewa gwamnan dai ya rigaya da zame kansa daga jam’iyyar saboda haka babu amfanin halartan taron.
KU KARANTA: Kotu ta dage shari'ar Sanata Jang da EFCC zuwa watan Oktoba saboda rashin shaida
Yace: “Ina tunanin gwamna Samuel Ortom ya yanke shawarar kansa; ya fota daga jam’iyyar APC; kuma mabiyansa basu ga amfanin halartan ganawar ba, dalilin da yasa ya ki amsa gayyatan kenan.”
Kamar yadda Legit.ng ta kawo muku, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana a ranan Litinin, 16 ga watan Yuli cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gidan gwamnatin jihar da ke garin Makurdi.
Ortom yayinda yake rantsar da sabon mai bashi sgawara na kananan hukumomi, Jerome Torshimbe, ya bayyana cewa an koreshi daga jam’iyyar APC
Yace: “ Game da jam’iyya kuwa, an koreni daga jam’iyyar. Ina waje yanzu. Kuma idan aka baiwa mutum jan kati, wannan na nufin cewa yanada na cewa na kansa.”
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng