Tabargaza: ‘Yan sanda sun rarumi wani likitan bogi bayan ya kashe mutum 2 da sunan tiyata

Tabargaza: ‘Yan sanda sun rarumi wani likitan bogi bayan ya kashe mutum 2 da sunan tiyata

- Dubun wani likitan bogi ta cika, 'yan sanda sun yi ram da shi

- Asirinsa ya dai tonu ne sakamakon aikin tiyata da yayi ma wasu marasa lafiya

Jami'an ma'aikatar lafiya na jihar Ondo tare da hadin gwiwar jami'an rundunar ‘yan sanda sun damke wani likitan bogi mai suna Adewale Emmanuel Owolanke a kauyen Uso da ke yankin karamar hukumar Owo.

Tabargaza: ‘Yan sanda sun rarumi wani likitan bogi bayan ya kashe mutum 2 da sunan tiyata
Tabargaza: ‘Yan sanda sun rarumi wani likitan bogi bayan ya kashe mutum 2 da sunan tiyata

Likitan bogin ana zarginsa ne da yiwa wasu majiyyata guda biyu aikin tiyata, wanda sanadiyyar hakan ya sa suka rasa rayukansu, sannan ya kuma kara jikkata wasu majiyatan da su ka zo neman lafiya gurinsa da ke zaune a yankin da ya ke.

Jawabin damke likitan na cikin wata sanarwa ne da jami'in hulda da manema labarai Abooluwa Famakinwa na ma'aikatar lafiya ta jihar Ogun ya sanyawa hannu.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: An kashe sama da mutum 500 a Filato, Nasarawa, Kogi, da Benuwai

Tun da farko ya bayyana cewa ma'aikatar lafiya ta jihar Ogun ta samu wani rahoto akan wata mata da likitan ya yiwa aikin tiyata, amma aka samu matsalar da ta kai majiyyaciyar ta tafi ga cibiyar lura da lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Owo, in da daga nan ne kwararrun likitoci suka gano dukkanin wanda ya yi wannan tiyatar hakika likitan bogi ne.

Bayan da aka damke likitan ne, yayi ta ikirarin cewa ya karanci aikin likitan ne a jami'ar Barbados, sabo da haka ya bude dan karamin asibiti mai ma'aikata guda uku.

Ma'aikatar lafiya ta jihar Ogun ta bayyana cewa dama an taba rufe wannan asibitin bisa laifin rashin kwarewar aiki.

A karshe kwamishinan lafiya na jihar Dr Wahab Adegbenro ya ce ma'aikatarsa za ta hukunta dukkanin wani wanda ya ke wasa da lafiyar bil' Adama, ta hanyar gurfanar da su a gaban kuliya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng