Ku saurari zuwanmu kwanan nan - Yan fashi sun aika wasika ga gauruwan Lagas

Ku saurari zuwanmu kwanan nan - Yan fashi sun aika wasika ga gauruwan Lagas

Tsoro da fargaba ya kama mutanen garuruwan Egan, Akesan da Igando bayan wasu yan fashi da makami sun aika da wata wasika gare su inda suke sanar da su batun ziyarar da za su kai masu.

An tattaro cewa barayin sun mammana wasikar a gaban wasu gidaje a garuruwan, inda suke sanar da su batun zuwansu yin fashi na kayyayakinsu.

An samu labarin cewa yan fashi sun taba kai hari garuruwan guda uku a baya, amma yan kato d agora da mazauna yankin suka dauka sun dakile harin nasu.

Ku saurari zuwanmu kwanan nan - Yan fashi sun aika wasika ga gauruwan Lagas
Ku saurari zuwanmu kwanan nan - Yan fashi sun aika wasika ga gauruwan Lagas

Ya ce: “Dukkaninmu dake yankin mun kwanta bacci cikin kwanciyar hankali, kawai muka tashi da safe muka ga an mammana fararen takardu a bangon wasu gidaje, ciki harda nawa.

“Abun mamaki ga kowa, yan fashin sun je har yankin Akesan da Igando inda suka manna irin wasikar a gidajen wurin, inda suke sanar da su zuwan nasu. A take muka sanar da yan sandan Igando.

KU KARANTA KUMA: An kashe yan sanda 4 sannan aka kona su kurmus a motar sintiri a Edo

“Yan sandan Igando sun bamu tabbacin lura da garuruwan da abun ya shafa. Bamu dogara das u kadai ba; mun debo yan banga domin lura da yankinmu. Sannan kuma muna fitowa da daddare muna taya yan bangan kula. Mafi akasarinmu dake Egan ba masu kudi bane; kawai muna dogaro ne ga Allah."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng