An sace dabbobi 36 yayinda aka nemi wani matashin makiyayi aka rasa a Plateau

An sace dabbobi 36 yayinda aka nemi wani matashin makiyayi aka rasa a Plateau

Jami’an tsaro a jihar Plateau na neman wani matashin makiyayi dan shekara 13 da wasu dabbobi 86 da aka sace a kusa da kauyen Bisichi sannan aka dauke su zuwa Foron dake karamar hukumar Barkin Ladi dake jihar a yammacin ranar Juma’a.

Ab tattaro cewa yaron na lura da dabbobin ne tare da wani babba amma aka neme su aka rasa bayan wanda ke tare da shi ya shiga kauyen Bisichi domin samo masu abun da za su ci.

Operation Safe Haven (OPSH), tawagar tsaron dake da hakkin kula da doka a jihar, a jiya tace an tura wata tawaga a yakin domin neman yaron da dabbobin da suka bata.

An sace dabbobi 36 yayinda aka nemi wani matashin makiyaya aka rasa a Plateau
An sace dabbobi 36 yayinda aka nemi wani matashin makiyaya aka rasa a Plateau

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ta fara harin Taraba da Gombe bayan lashe zaben Ekiti

Jami’in labarai, Manjo Adam Umar ya fadama majiyarmu a kan waya cewa sakataren MACBAN na Barkin Ladik ne ya kai rahoton lamarin sannan kuma tawagar dake bincike sun hada da jami’an tsaro da mazauna yankin da suka san hanya.

Sakataren MACBAN a Barkin Ladi, Abubakar Gambo ya bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 5:00 na yamma sannan kuma cewa sahun dabbobin ya nuna cewa an kai su Foron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng