Bayan shekaru da dama, Obasanjo ya fadi dalilin da ya sa ya fice daga PDP

Bayan shekaru da dama, Obasanjo ya fadi dalilin da ya sa ya fice daga PDP

Tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP a da, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga jam'iyyar kimanin sama da shekaru hudu da suka shude.

Cif Obasanjo ya bayyana dalilin na sa ne a yayin da yake tattaunawa da shugabannin jam'iyyar da suka kai masa ziyasa a ranar Asabar din da ta gaba.

Bayan shekaru da dama, Obasanjo ya fadi dalilin da ya sa ya fice daga PDP
Bayan shekaru da dama, Obasanjo ya fadi dalilin da ya sa ya fice daga PDP

KU KARANTA: Bayan faduwa zabe, za'a kai Fayose kotu

Legit.ng ta samu cewa Obasanjo ya bayyana cewa babban dalilin ficewar sa jam'iyyar shine yadda wani gwamna a karkashin inuwar ta ya rika zagin sa yana ci masa mutunci amma aka kasa hanashi.

Ya bayyana hakan a matsayin abunda yayi masa ciwo sosai da takaici.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin manyan jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa National Electoral Commission, INEC kuma kwamishinar da ke kula da harkokin zabe da tafiyar da ayyuka Hajiya Aminat Zakari ta ba gwamnan jihar Ekiti mai barin gado kwana biyu ya bata hakuri ko kuma su hadu kotu.

Kwamishinar dai ta ba shi wa'adin ne biyo bayan zargin da yayi mata tare da wasu mutanen da jami'an tsaro ta hada baki da 'yan siyasa a jihar wajen murde zaben da aka gudanar na gwamna a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng