An sanar da ranar fara jigilar mahajjatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki
Hukumar nan dake da alhakin jin dadi da walwalar mahajjatan Najeriya mallakin gwamnatin tarayya watau National Hajj Commission (NAHCOM) a takaice ta saka ranar 21 ga wannan watan na Juli a matsayin ranar fara jigilar mahajjata zuwa kasa mai tsarki.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar ya fitar wakilin wannan jaridar ya kuma gani.
KU KARANTA: "Jam'iyyar PDP tamkar aljannace a Najeriya"
Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar, hukumar ta kuma bayyana ranar 18 ga wannan watan din dai a matsayin ranar rufe karbar kudin zuwa hajjin daga mahajjatan kasar.
A wani labarin kuma, Shugaban majami'un darikar Roman Katolika na garin Abuja, babban binin tarayya mai suna John Cardinal Olaiyekan ya bayyana cewa bishop-bishop din Najeriya tuni suka yanke kauna da samun shugabanci na gari daga shugaba Buhari.
John Cardinal ya bayyana hakan ne a garin Ilorin na jihar Kwara lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala nadin shugaban majami'un Roman Katolikan jihar Bishop Paul Olawoore.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng