Da dumin sa: Shugaba Buhari ya jawo Ali Modu Sheriff kusa da shi da wani muhimmin mukami
Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu da dama shine shugaban kasar Najeriya ya nada tsohon gwamnan jihar Borno, kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na rikon kwarya Ali Modu Sheriff a matsayin daraktan kwamitin neman goyon baya a zaben dake tafe na 2019.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar nadin da Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya sanya wa hannu a madadin shugaban kasar.
KU KARANTA: Sunayen tsaffin gwamnoni 13 za Buhari ke shirin kwacewa kadarori
Legit.ng ta samu cewa shi dai wannan kwamitin ya sha ban-ban ne da Buhari Campaign Organisation (BCO) wanda a baya aka nada Ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin shugaba.
A baya dai anyi ta zargin cewa Ali Modu Sherif yana da hannu a cikin kungiyar nan ta ta'addanci ta Boko Haram.
A wani labarin kuma, Babban bankin duniya ya nada wani matashi mai suna Muhammad Abdullahi dake zaman kwamishinan tsare-tsare da kuma kasafin kudin gwamnatin jihar Kaduna a matsayin mamaba a majalisar ta mu'amala da mutane watau Expert Advisory Council on citizen engagement a turance.
Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta DailyNigerian, Mista Muhammadu Abdullahi, kwararre ne a harkokin tattalin arziki kuma yanzu zai hadu ne da wasu mutane biyar daga sassa daban-daban na duniya domin yin aikin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng