Kashe-kashe: Lokaci yayi da Buhari zai tattara ya bar ofis – ‘Dan Majalisar APC

Kashe-kashe: Lokaci yayi da Buhari zai tattara ya bar ofis – ‘Dan Majalisar APC

Mun samu labari cewa wani ‘Dan Majalisa daga Yankin Arewawacin Najeriya ya bayyana cewa lokaci yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai hakura ya tattara ya bar mulkin kasar nan.

Kashe-kashe: Lokaci yayi da Buhari zai tattara ya bar ofis – ‘Dan Majalisar APC

Wani ‘Dan Majalisar APC yace Buhari ya ajiye aiki saboda kashe-kashen da ake yi

Dan Majalisar Gwarzo da Kabo a Majalisar Wakilan Tarayya karkashin Jam’iyyar APC mai mulki Hon. Nasiru Sule Garo ya nemi Shugaba Buhari ya sauka daga kujerar Shugaban kasar ne saboda kashe-kashen da ake yi a Najeriya.

Kwanan nan ne aka kashe sama da mutum 40 ana zaman lafiya a cikin wani Gari a cikin Sokoto. Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya yayi jawabi inda ya kuma shan alwashin ganin karshen wannan ta’adi da ake yi a kasar.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan APC ya gargadi Jam'iyya mai mulki

Sai dai ‘Dan Majalisar wanda yake bangaren rAPC yace sun gaji da jin gafara sa ba su ga kaho ba don haka Shugaban kasan ya hakura da mulkin ya bada wuri. ‘Dan Majalisar yayi wannan bayani ne ta shafin sa na Tuwita a jiya.

Honarabul Sule Garo ya yaba da kokarin Shugaba Buhari amma yace ya kamata ya wani wuri ya zo ya mulki kasar. Garo dai yaron tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Kwankwaso ne tun kafin ya samu zuwa Majalisar.

Dazu kun ji cewa ‘Dan Majalisar wanda yake tare ‘Yan aware na Jam’iyyar APC da ke karkashin rAPC yace bai ji dadin abin da Jami’an tsaro su kayi a Ekiti ba kuma zai so ya ga PDP tayi nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel