Yaki da rashawa: Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015 - Inji PDP
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta bayyana cewa shugaban kasar Najeriya baya da wata kima ko kwarjinin da zai zo yana ta faffaka game da yaki da cin hanci da rashawa idan dai har bai binciki inda kudaden kamfe din sa na 2015 suka fito ba.
Wannan kalamin dai sun fito ne daga ofishin babban sakataren yada labarai na jam'iyyar ta PDP Kola Olagbondiyan a yayin wani taron jam'iyyar a jihar Kogi.
KU KARANTA: An ce INEC ta canza jadawalin zabe albarkacin ranar Arfa
Legit.ng ta samu cewa Mista Kola ya ce abun takaici ne yadda shugaban ke fitowa yana ta kumfan baki game da yaki da cin hanci da rashawa amma kuma a dayan bagaren yana zagaye da barayi.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal ya yi tsokaci tare da tambihi mai daukar hankali a game da kashe-kashen da ke aukuwa a kusan dukkan sassan kasar nan inda ya bayyana cewa ba abun da talakawan kasar suka zaba ba kenan a shekarar 2015.
Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake nuna alhinin sa akan mutane sama da 30 da wasu 'yan bindiga suka kashe a kauyen karamar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng