Dalilai 5 da ke haddasa mace-macen aure

Dalilai 5 da ke haddasa mace-macen aure

Mace-macen aure matsala ne da ya yawaita musamman a kasar Hausa. Anyi ittifakan cewa jihar Kano na da yawan zawarawa manya da kananan yara.

Ga wasu daga cikin dalilan da ake ganin suna haifar da wannan matsala:

1. Jahilci: Matsala ta farko da take jawo mace macen aure a kasar hausa a wannan zamani itace jahilci da yawan mutanen mu, musamman mutanen kauyuka, mun jahilci menene aure a mu’amalance da kuma a Addinance. Da yawan matasa da suke aure a yanzu yawancin su basu san ma’anar aure ba, basu san ka’idojin aure ba, basu san hukunce hukuncen aure ba, kai wallahi wasu ma basu san ya ake yin wankan Janaba ba, amma a haka suke zuwa neman aure kuma a basu.

2. Kwadayi: Hausawa dai suna cewa “idan har da kwadayi, to da wulakanci”, kuma kowa ya hau motar kwadayi to zai sauka a tashar wulakanci. sannan kuda wurin kwadayi yake mutuwa. Da yawan mace macen auren da ke faruwa a kasar Hausa suna biyo bayan kwadayi ne da a’auratan suke sawa a cikin zukatan su tun kafin suyi auren.

3. Auren dole na daga cikin abubuwan dake kawo yawan mace-macen aure musamman a kasar Hausa inda abun ya zamo ruwan dare.

4. Auren Zumunci idan yayi kyau yafi komai dadi, idan kuma ya baci yafi komai muni. Irin wannan aure kan yi karko ne kawai idan ma'auratan ne suka hada kansu.:

KU KARANTA KUMA: Budurwa mai Digiri 2 mai shekaru 40 ta kashe kanta a saboda an dame ta tayi aure

5. Auren Sha’awa: Auren sha’awa dai shi ne mutum ya yi aure domin kyawun jiki ko surar dan uwansa, illar irin wannan auren shi ne; da zarar wadannan Suffofi da akayi auren domin su suka gushe,to shikenan matsala zata fara aukuwa a auren daga nan sai rabuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng