Marigayi Audu Abubakar ne ya bamu bindigogi – Yan fashi
Rundunar yan sandan jihar Kwara tare da sashin kwararru na IGP sun kama wata tawaga na yan fashi guda hudu, wadda suka kware wajen kai hari tashoshin man fetur a jihar Kwara da kewayenta.
Legit.ng ta tattaro cewa Aminu Pai Saleh, kwamishinan yan sandan jihar, da yake Magana da manema labarai a Ilorin a ranar Talata, 10 ga watan Yuli, bayan gurfanar da yan fashin, ya bayyana cewa shugaban su James Obaje mai shekaru 34, dan asalin Dekina dake karamar hukumar Dekina na jihar Kogi ya bayyana cewa shi dan fadar wani Zakari Yau, Karen yan sisaya a jihar Kogi.
A lokacin hira da manema labarai, shugaban kungiyar, yace bindigogin AK47, da na K2 da sauran bindigogin da aka samu a hannunsu ba kowa bane ya mallaka mashi su ba face tawagr yakin neman zaben marigayi dan takarar gwamnan APC a jihar Kogi, Alhaji Abubakar Audu a lokacin zabe.
KU KARANTA KUMA: Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari
A cewar shugaban yan sandan, sauran yan kungiyar sun hada da Nelson Yakubu shekara 31, Ibrahim Mutari shekara 33 da kuma Gboyega Olaoye shekara 35.
Ya kuma kara da cewa dukkaninsu yan jihar Kogi ne amma suna zaune a Ilorin banda Gbenga Olaoye wanda ya fito daga karamar hukumar Ekiti na jihar Kwara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng